Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Aldastur ta kasar Jordan an habarta cewa, an bude wasu cibiyoyin hardar kur'ani mai tsarki 144 a lardin Akbah na kasar Jordan, inda ake yin amfani da su domin bayar da horo hardar kur'ani ga matasa. Bayanin ya ci gaba da cewa daga cibiyoyin an ware wasu hamsin da uku domin bayar da horon harda ga mata. 604535