Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran bernama na kasar Malazia cewa, an kafa wani sabon kwamiti da zai gudanar da ayyukan samar da kudaden kasa da kasa na kasashen musulmi a kasar Malazia, domin yin nazari kan hanyoyim hakan. Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka kwamiti ya fara gudanar da zamansa domin tattaunawa tsakanin mambobinsa kan muhimman batutuwa da suka shafi harkokin tattalin arziki da cinikayya, da kuma yadda zasu fara gudanar da ayyukansu.606597