IQNA

Zaman Taro Kan Harkokin Tattalin Arzikin Kasashen Musulmi A Tehran

14:30 - July 05, 2010
Lambar Labari: 1951552
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da zaman taro a matsayi na kasa da kasa kan harkokin bunkasa tattalin arzikin kasashen musulmi a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na itsr.ir an bayyana cewa Za a gudanar da zaman taro a matsayi na kasa da kasa kan harkokin bunkasa tattalin arzikin kasashen musulmi a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da halartar wakilai daga kasashen musulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannnan taro za a gudanar da shi ne a cikin watanni uku masu zuwa, wanda kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen musulmi ta CARSICM ta shirya gudanarwa. Ya kara da cewa yanzu haka an kamamla mafi shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da wannan zaman taro.

Daga cikin muhimman abubuwan da zaman taron zai mayar da hanakali kansu akwai samar da hanyoyi na dogaro da kai wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi a nan gaba.

609045





captcha