Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na Nils ya bayyana cewa, kwamitin yaki da nuna wariya ga wani jinsin mutane da kyamar baki a nahiyar turai ya fitar da bayani da ke cewa dukkanin abubuwan biyu suna ci gaba karuwa a cikin nahiyar turai musamman ma a cikin 'yan lolkutan nan.
A cikin bayanin da kwamitin ya fitar a jiya ya yi ishara da cewa, al'ummar nahiyar turai tana kara nisantar abin da aka santa da shia a lokutan baya na karbar al'adu daga sassa daban-daban na duniya, lamarin da shi ne ya bata damar samun ci gaba abangarorin rayuwa.
Haka nan kuma bayanin ya tabbatar da cewa wadanda suka fi fuskantar matsala a halin yanzi a cikin kasashen nahiyar turai musulmi da suka fito daga kasashen larabawa ko kasashen nahiyar Afirka, inda ake nuna musu wariya da kyama da wuce duk wani haddi na 'yan adamtaka.
612363