IQNA

Za A Fara Koyar Da Darussan Musulunci A Jami'oin Jamus

20:38 - July 15, 2010
Lambar Labari: 1956239
Bangaren kasa da kasa; Minista mai kula da harkokin ilmi mai zurfi a kasar Jamus Annette Schavan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a fara koyar da wasu darussa na addinin Musulunci a wasu jami'oin kasar Jamus.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na samanyo na yanar gizo an habata cewa, minista mai kula da harkokin ilmi mai zurfi a kasar Jamus Annette Schavan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a fara koyar da wasu darussa na addinin Musulunci a wasu jami'oin kasar Jamus, da nufin kara wayar da kan al'ummar kasar kan addinin Musulunci.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka an kammala shiri koyar da wasu darussa na addini Musulunci, ta yadda hakan zai bayar da dama masu nazari na kasar jamus musamman kan addinai, su kara samun masaniya kan addinin Musulunci da mahangarsa kan lamurra da daman a ilimi, da kuma rayuwa da tsarinsa a cikin dukkanin lamurra.

614211



captcha