Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga Isesco ta watsa rahoton cewa; ; hukumar da ke kula da koyar da matasa da fadakarwa kan al'adun Musulunci Essesko a ranekun shidda zuwa sha biyar ga watan Murdad na wannan shekara za bawa matasa horo na musamman da tattaunawa da su a kauyen ilimin na Tunusiya wato ITE DES SCIENCES DE TUNIS. A gurin wannan taro za a samu halartar kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa da kasa kamar kungiyar kasa da kasa mai lura da harshen faransanci a dunbiya OIF tare da hadin guiwar ma'aikatar da ke kula da matasa da al'amuran wasanni a kasar Tunusiya tare da halartar matasa sama da dari musulmi da wadanda ba musulmi ba daga kasashe mambobi a Isesco da kuma daga kasar Faransa.
615149