IQNA

An Bude Tashar Talabijin Din Musulunci A Afirka Ta Kudu

15:10 - July 21, 2010
Lambar Labari: 1960079
Bangaren kasa da kasa; An bude wata tashar talabijin ta Musulunci mai suna Islamic TV akasar Afirka ta kudu, wadda cibiyar kula da harkokin sadarwa ta kasa da kasa Playbox Technology ta bude, kuma za ta fara gudanar da ayyukanta.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na rfv an habarta cewa, an bude wata tashar talabijin ta Musulunci mai suna Islamic TV akasar Afirka ta kudu, wadda cibiyar kula da harkokin sadarwa ta kasa da kasa Playbox Technology ta bude, kuma za ta fara gudanar da ayyukanta daga ranar Asabar mai zuwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tashar talabijin za ta mayar da hankali wajen gabatar da shirye-shirye da suke da dangantaka da addinin Musulunci, kama daga lamurra da suka danganci zamantakewa, ilmomi da dai dai sauransu.

Daga cikin muhimman ayyukan tashar har da gabatar shirye-shirye na wayar da kai kan koyarwar addinin musulunci a kan hakkokin dan adam, da kuma kyawawan dabi'u da kuma shirye-shirye da suka shafi tarbiyar iyali.

618271



captcha