Bangaren kasa da kasa; An buga tare da watsa littafin ayyukan hajji da wani marubuci kuma dan shi'a kasar Saudiyya ya wallafa, wanda ya bayyana muhimman abubuwan da ya kamata ayi la'akari da su yayin gudanar da ayyukan hajji.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga shafin cibiyar kula da harkokin kur'ani ta Muzn cewa, an buga tare da watsa littafin ayyukan hajji da wani marubuci kuma dan shi'a kasar Saudiyya ya wallafa, wanda ya bayyana muhimman abubuwan da ya kamata ayi la'akari da su yayin gudanar da ayyukan hajji da sauran ayyukan ibadu da suke da dangantaka da shi.
Bayanin ya ci gaba da cewa Allamah Sheikh Hussain Ali Mustafa shi ne ya rubuta littafin, yayin da babban malamin Ayatollah sheikh Abdulhadi Fadli ya yi masa gabartawa.
Malamin ya yi kokari a cikin littafin wanda ya wallafa a cikin mujalladi biyar wajen bayyana matsayin aikin hajji a Musulunci, da kuma yadda ake aiwatar da shi gami da dalilai da annasosi.
618924