IQNA

Ana Nuna Wani Kur'ani Mai Shekaru 1000 A Birnin Dubai

17:58 - July 22, 2010
Lambar Labari: 1960419
Bangaren kasa da kasa; Ana nuna wani kur'ani da aka rubuta shekaru 1000 da suka gabata a birnin Dubai an hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar kula da harkokin al'adu Barjaman ta dauki nauyin gabatarwa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Ittihad ta kasar hadaddiyar daular larabawa an habarta cewa, ana nuna wani kur'ani da aka rubuta shekaru 1000 da suka gabata a birnin Dubai an hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar kula da harkokin al'adu Barjaman ta dauki nauyin gabatarwa tare da shiryawa a birnin.

Bayanin ay ci gaba da cewa wannan kur'ani dai an fi saninsa da mushafin ibn Bawwab, kuma nauin rubutunsa irin Alhasan Hilmi, wanda kasar take yin alfahari da shi a matsayin wani abin tarihi mai girma a kasar.

Za 'a kammala wannan baje kolin nuna mafi dadewar ku'ari a kasar haaddiyar daular laraba a karshen watan nan da muke ciki, wanda ke samun halartar manazarta daga kasashen duniya.

618881


captcha