Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wabi zaman taro na tunawa da babban malamin addinin na kasar Labanan Allamah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah a birnin Tehran, da zai samu halartar manyan malamai na kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa alkausar ya habarta cewa, Za a gudanar da wabi zaman taro na tunawa da babban malamin addinin na kasar Labanan Allamah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah a birnin Tehran, da zai samu halartar manyan malamai na kasar.
Daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hakalin kansu akwai batutuwa da suka shafi matsayinsa na gwagwarmaya da zaluncin duniya, musamman ma gwagwarmayar al'ummar labanan da haramtacciyar kasar Isra'ila.
A bangare guda kuma taron zai dubi kan matsayinsa na ilmi da kuma rubuce-rubucen day a yi domin amfanin al'ummar musulmi baki daya.
618715