IQNA

Allamah Sayyid Fadlollah Ya Kasance Ma'abucin Tattaunawa

14:42 - July 24, 2010
Lambar Labari: 1961327
Bangaren kasa da kasa; A taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran kan marigayi Ayatollah Sayyid Mohammad Hussain Fadlollah, an bayyana malamin a mtsayin babban malamin addini day a bayar da muhimmanci ga tattaunawa tsakanin addinai dmin samun fahimtar juna.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta, A taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran kan marigayi Ayatollah Sayyid Mohammad Hussain Fadlollah, an bayyana malamin a mtsayin babban malamin addini day a bayar da muhimmanci ga tattaunawa tsakanin addinai dmin samun fahimtar juna da kuma samun lafiya tsakanin dukkanin al'ummomi.

A cikin bayanin jagoran juyin juya halin musulunci da aka karanta a wajen taron, ya bayyana rashin Allamah Fadlollah a matsayin rashi na al'ummar musulmi baki daya, domin kuwa rashin Fadlollah a cikin musumi rashi ne mai girma da cike gurbinsa abu ne mai matukar wahala.

Babban dansa ya bayyana a wajen taron cewa, mahaifinsa ya kasance daya daga cikn mutanen da suke kare juyin juya halin musulunci a baki dayan rayuwarsa, kuma bai gushe kan hakan ba har ya bar duniya.

619769








captcha