Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a jami'ar birnin Salzburg na kasar Austria, da zai yi dubi kan mahangar musulunci dangane da hakkkin dan adam a dukkanin bangarrin rayuwa ta zamantakewa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalt daga shafin sadarwa na yanar gizo na salzglobal an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a jami'ar birnin Salzburg na kasar Austria, da zai yi dubi kan mahangar musulunci dangane da hakkkin dan adam a dukkanin bangarorin rayuwa ta zamantakewar jama'a.
Zaman taron har wala yau zai dubi kan batutuwa da suka danganci matsayin musulmin nahiyar turai da kuma yadda ake yin mu'amala da su, da kuma yadda suke neman a kare hakkokinsu.
619818