Bangaren kasa da kasa; Aya ta 7 a cikin surat ra'ad ta bayyana cewa kowace jama;a na da mai shiryazwa, a cikin kowace jama'a akwai jagora shugaba da za a koma zuwa gare s hia cikin dukkanin lamurra, jagoran wannan al'umma shi ne Mahdi (AS)
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a taron mahdawiyya karo na shida da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa, wakilin kwamitin mabiya ahlul bait a kasar Birtaniya ya bayyana cewa, aya ta 7 a cikin surat ra'ad ta bayyana cewa kowace jama;a na da mai shiryazwa, a cikin kowace jama'a akwai jagora shugaba da za a koma zuwa gare s hia cikin dukkanin lamurra, jagoran wannan al'umma shi ne Mahdi (AJ) wanda ake jiran bayyanarsa.
Ya kara da cewa dukkanin al'ummomi sun yi imani da cewa a karshen duniya wani mutum salihi zai bayyana domin kare al'umma daga zaluncin masu zalunci, da jabberancin masu jabberanci.
Yayin da al'ummar musulmi ta yi imani da cewa ba kowane illa Imam Mahdi (AS) wanda manzon Allah (SAW) ya yi al'ummarsa alkawalin bayyanarsa a karshen zamani, a lokacin da aka cika duniya da zalunci da danniya.
620430