IQNA

Rijistar Sunayen Masu Shiga Gasar Kur'ani A Saudiyya

19:43 - July 25, 2010
Lambar Labari: 1962101
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da rijistar sunayen masu shiga gasar hardar kur'ani mai tsarki da za a gudanar a yankin Saihat na kasar Saudiyya a cikin watan Ramadan mai zuwa da za ta kebanci mata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin tashar sadarwa ta Rasid an bayyana cewa, An fara gudanar da rijistar sunayen masu shiga gasar hardar kur'ani mai tsarki da za a gudanar a yankin Saihat na kasar Saudiyya a cikin watan Ramadan mai zuwa da za ta kebanci mata daga cikin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) da ke yankin.

Bayanin ya kara da cewa yanzu haka daruruwa daga cikin mahardata sun riga sun yi rijistar sunayensu, kuma za akammala rijistar sunayen ne a cikin mako na sama, kuma za a fara gudanar da gasar ne a cikin wata azumi mai zuwa.

620272
captcha