IQNA

Ana Bayar Da Horon Hardar Kur'ani A Birnin Bagdad

19:44 - July 25, 2010
Lambar Labari: 1962104
Bangaren kasa da kasa; Makarantar koyar da karatu da ilmomin kur'ani mai tsarki ta Alhuda dake birnin Bagadaza na ci gaba da gudanar da horon hardar kur'ani mai tsarki a hutun bazara da ake ciki a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na Muzni ya bayyana a cikin shafinsa na yanar gizo cewa, makarantar koyar da karatu da ilmomin kur'ani mai tsarki ta Alhuda dake birnin Bagadaza na ci gaba da gudanar da horon hardar kur'ani mai tsarki a hutun bazara da ake ciki a kasar Iraki baki daya.

Shugabar makarantar Alhuda ta birnin Bagadaza ta bayyana cewa, wannan shirin shi ne irinsa na farko da aka fara gudanarwa da irin wannan salo a makarantar, da nufin bayar da dama ga dalibai mata da suke da ikon hardar kur'ani mai tsarki su samu ingantaccen horo kan hakan.

620233
captcha