Bangaren siyasa da zamantakewa; kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar biyu ga watan Murdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ta yi amanna da yin maraba da matakin babban kotun duniya da majalisar dinkin duniya na amincewa da Kosovo a matsayin kasa mai yanci inda ta samu yancinta daga Sabiya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta daga yankin Balkan bayan ta nakalto daga jaridar Alsharuk da ke fitowa daga kasar Masar ta watsa rahoton cewa; ; kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar biyu ga watan Murdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ta yi amanna da yin maraba da matakin babban kotun duniya da majalisar dinkin duniya na amincewa da Kosovo a matsayin kasa mai yanci inda ta samu yancinta daga Sabiya. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar da wani bayani ne da a cikinsa ta ke cewa Ikmalul Din Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar ta hadin kan kasashen musulmi ya yi imani cewa wannan hukunci ya yi daidai da bukatar al'ummar Kosovo kuma al'ummar Kosovo sun cancanci a bas u kasa ta su ta kansu domin gina kansu da kansu.
621081