IQNA

Shirin Bayar Da Horo Kan Hardar Kur'ani A Birnin Sharjah

18:57 - July 26, 2010
Lambar Labari: 1962480
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da shirin bayar da horo na musamman kan hardar kur'ani mai tsarki a karo na biyu a birnin Sharjah na kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar ta shirya gudanarwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Albayan an habarta cewa, an fara gudanar da shirin bayar da horo na musamman kan hardar kur'ani mai tsarki a karo na biyu a birnin Sharjah na kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar ta shirya gudanarwa a cikin lokutan nan.

Hassan Abdulrahman Al-sa'ab shi ne ya sanar da hakan a zantawar da ta hada shi da manema labarai a birnin Sharjah, inda ya ce yanzu shirin na gudanar kamar yadda ya kamata, kuma matasa na samun horon harda kamar yadda aka shirya.

620895



captcha