IQNA

Jam'iyar Republican Australia Ba Ta Goyon Bayan Masu Sukar Musulunci

13:42 - July 28, 2010
Lambar Labari: 1963303
Bangaren kasa da kasa; Jam'iyar Republican a kasar ta fito karara ta bayyana cewa ba ta goyon bayan 'yan takara masu sukar addinin Musulunci, a kan haka ne ma ta dakatar da dan takara mai sukar Musulunci daga jam'iyar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Al-nadwa ta kasar Saudiyya cewa, jam'iyar Republican a kasar ta fito karara ta bayyana cewa ba ta goyon bayan 'yan takara masu sukar addinin Musulunci, a kan haka ne ma ta dakatar da dan takara mai sukar Musulunci daga jam'iyarda ke shirin shiga zabe.

Dan takarar na jam'iayr Republican David Parkar wanda ke tsananin ra'ayin gaba da addinin Musulunci ya bayyana cewa, jam'iya mai mulki a kasar tana kokarin mika wa musulmi kasar Australia, a kan haka idan ya lashe zabe zai shiga kafar wando daya da musulmi.

Wanna furuci nasa ya bakanta manyan jam'iyar, inda suka dauki matakin dakatar da shi nan take, tare da bayyana musulmi a matsayin mutane kamar kowa.

621998


captcha