Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tawagar iqna a gasar kur'ani ta Malazia ta habarta cewa, gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da za a fara gudanarwa a birnin Kualalampor na kasar Malazia za ta samu halartar alkalan gasa daga kasashe goma sha daya domin sanya idon kan yadda gasar za ta kasance tare da bayar maki ga masu karatu da harda da sauran bnagarorin gasar.
Shugaban kwamitin alkalan da za su alkalanci a gasar Muhammad Sheikh Abdulaziz ya bayyana cewa dukkanin alkalan za su fara gudanar da zama kafin fara gudanar da gasar.
Ya ce suna da bukatar su san komai dangane da shirye-shiryen gasar, ta yadda za su gudanar da alkalancinsu bisa masaniya kan dukkanin bangarorin da gasar za ta shafa.
622527