Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da jaridar alyaum sabi ta kasar Masar ta buga a shafinta na yanar gizo ta bayyana cewa, za a bude wani babban dakin ajiye kayayyakin tarihin Musulunci a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, wanda kasashe goma sha hudu suka hada karfi wajen sake gyara shi tare da kawata shi.
Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar kula da harkokin al'adu ta kasar Masar ita ce ta shiga gaba wajen gudanar da aikin, tare da taimakon wasu kasashen musulmi.
Yanzu haka dai an kammala dukkanin ayyukan gyaran wannan babban dakin kayan tarihin Musulunci, wanda ya lakume tsabar kudi har lira miliyan casa'in.
623367