Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Alkausar ta watsa rahoton cewa; ; babbar kotun koli ta musamman da ta shafi harkokin tsaro a kasar Masar ta yi watsi da hukumcin yin awangaba da Muhammad Faruk Muhammad Alsaid fitaccen dan shi'a a wannan kasa ta Masar da ake zargi da yada mazhabar shi'a a wannan kasa. Wannan hukumce matukar aka yi aiki da shi zai kara daidaita lamuran addini a wannan kasa kuma zai rage nuna banbancin da ake nuna wa wasu mabiya addinin Musulunci a wannan kasa.
623290