IQNA

Za A Fara Gudanar Da Baje Kolin Littafan Iran A Karbala

9:42 - August 01, 2010
Lambar Labari: 1964681
Bangaren kasa da kasa; A yau lahadi za a fara gudanar da kasuwar baje kolin littafan kasar Iran a birnin Karbala mai alfarma, wanda cibiyar bunkasa harkokin ilmi da ala'adu ta jamhuriyar musulunci ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar kula da bunnakasa harkokin al'adu da ilimi cewa, a yau lahadi za a fara gudanar da kasuwar baje kolin littafan kasar Iran a birnin Karbala mai alfarma, wanda cibiyar bunkasa harkokin ilmi da ala'adu ta jamhuriyar musulunci ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin mai alfarma.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan dai ba shi ne karon farko da ake gudanar da irin kasuwar baje koli ta madaba'antun kasar Iran a kasar Iraki ba, amma a wannan karon baje kolin zai samu halartar cibiyoyin buga littafai da dama.

623861
captcha