IQNA

Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Na UN Ya Yi Suka Kan Killace Gaza

9:41 - August 01, 2010
Lambar Labari: 1964682
Bangaren kasa da kasa; Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dindin duniya ya yi kakkausar suka kan ci gaba da killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra'ila ta ke yi, tare da yin kira da a kawo karshen killace yankin.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran reauters cewa, kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dindin duniya ya yi kakkausar suka kan ci gaba da killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra'ila ta ke yi, tare da yin kira da a kawo karshen killace yankin na Gaza.

Bayanin y ace a koda yaushe haramtacciyar kasar Isra'ila tana yin watsi da dukkanin kudurori na majalisar dinkin duniya, wanda hakan ba za ataba yarda da shi ba.

Kwamitin y ace dole haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya ta yi aiki da dukkanin kudurorin majalisar dinkin ba tare da gabatar da wani uzuri ba, hakan ne kawai zai fitar da ita daga ayyukan da take aikatawa da suka saba wa doka.

623857
captcha