Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na musulmin kasar Faransa na yanar gizo an habarta cewa, a ci gaba da gudanar da wani baje kolin littafai da ake gudanarwa akasar faransa an nuna wasu daga cikin liffan da babban malamin falsafar nan dan kasa Iran Bu Ali Sina ya rubuta a bnagarori daban-daban na ilimi, musamman ma bangaren likitanci.
Bayanin ya kara da cewa wannan baje koli na daya daga cikin manyan baje kolin littafan musulunci da akan gudanar a kasar Faransa tare da halartar madaba'antu daga kasashen musulmi.
Rahoton ya ci gaba da cewa yanzu wasu daga cikin madaba'antun kasar Iran suna ci gaba da halartar wannan baje koli, inda nuna littafan Bu Ali Sina.
624154