IQNA

Manyan malaman Najaf Na Karfafa Gina Cibiyoyin Kur'ani

14:22 - August 02, 2010
Lambar Labari: 1965767
Bangaren kasa da kasa; Manyan malaman addinin Musulunci na kasar Iraki da ke birnin Najaf mai alfarma sun nuna goyon bayansu ga ci gaba da gina cibiyoyin koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki a fadin kasar Iraki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da hada wakilinsa a kasar Iraki da daya daga cikin malaman kur'ani kuma babban daraktan cibiyar kur'ani ta birnin Najaf Adnan Rad ya bayyana cewa, Manyan malaman addinin Musulunci na kasar Iraki da ke birnin Najaf mai alfarma sun nuna goyon bayansu ga ci gaba da gina cibiyoyin koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki a fadin kasar.

Malamin ya kara da cewa bisa la'akari da muhimmancin da ke tattare da koyar da ilmomin kur'ani a makarantu da sauran cibiyoyin ilimi, manyan malaman addinin na birnin Najaf suka mayar da hankali wajen karfafa gina cibiyoyin koyar da kur'ani.

Daga lokacin da aka kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Iraki Saddam Hussain ya zuwa yanzu an gina daruruwan cibiyoyin koyar da kur'ani a kasar, musamamn ma a yankunan kudanci.

624012


captcha