IQNA

Tashar Alkausar Tana Taka Gagarumar Rawa A baje Kolin Karbala

15:47 - August 02, 2010
Lambar Labari: 1965867
Bangaren kasa da kasa; Tashar alkausar da ke watsa shirye-shiryenta a cikin harshen larabci daga kasar Iran tana taka gagarumar rawa a taron baje kolin kayyakin al'adu da ke gudana a birnin Karbala mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton da ya nakalto daga shafin sadarwa na yada al'adun kasar Iran an bayyana cewa, tashar alkausar da ke watsa shirye-shiryenta a cikin harshen larabci daga kasar Iran tana taka gagarumar rawa a taron baje kolin kayyakin al'adu da ke gudana a birnin Karbala mai alfarma na kasar Iraki.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje koli ana gudanar da shi kan kayayyakin da suka danganci harkokin al'adu na Musulunci a kasashen musulmi da na larabawa, wanda ke samun halartar wakilai daga kasashe daban-daban.

A bangare guda kuma baje kolin ya shafi littafai na addini da aka buga kan maudu'ai da suke da dangantaka da addinin Musulunci, al'adu siyasa zamantakewa da dai sauransu.

Da dama daga cikin madaba'antu na kasar Iran sun kai littafai da aka buga da nufin amfanar da al'ummar musulmi, wanda hakan zai karfafa hadin kai tsakanin wannan al'umma.

624436

captcha