IQNA

Gyarawa Tare Da Sake Gina Wuraren Tarihin Musulunci A Muzambiq

16:07 - August 03, 2010
Lambar Labari: 1966607
Bangaren kasa da kasa; Wata kungiyar malaman jami'a da suka hada musulmi da mabiya addinin kirista suna gudanar da ayyukan gyaran wuraren tarihin Musulunci a kasar Muzambiq, da suka hada da makarantu gami da cibiyoyin ilimi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga samanyolurhaber an bayyana cewa, wata kungiyar malaman jami'a da suka hada musulmi da mabiya addinin kirista suna gudanar da ayyukan gyaran wuraren tarihin Musulunci a kasar Muzambiq, da suka hada da makarantu gami da cibiyoyin ilimi da dai sauransu.

Wannan cibiya tana gudanar da wadannan ayyukan ne bisa la'akari da cewa addinin Musulunci daya ne daga cikin manyan addininai da suke da tasiri a kasar.

An kafa kungiyar net un a cikin shekara ta 1991, kuma tana gudanar da ayyukan nata ne a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Da dama daga cikin mabiya addinin Musulunci na kasar Muzambiq musulmi ne mazauna yankunan gabacin Afirka, da kuma larabawa da ke makwaftaka da nahiyar.

625161
captcha