IQNA

Za A Gudanar Da Taron Bude Babbar Agogon Duniya A Makka

19:53 - August 05, 2010
Lambar Labari: 1967451
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da taron bude wani katafaren gini da ke dauke da agogo mafi girma a duniya a birnin Makka mai tsarki, wanda za a gudanar a ranar daya ga watan Ramadan mai kamawa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakallto daga shafin yanar na jaridar kasar Saudiyya ta al-watan an bayyana cewa, za a gudanar da taron bude wani katafaren gini da ke dauke da agogo mafi girma a duniya a birnin Makka mai tsarki, wanda za a gudanar a ranar daya ga watan Ramadan mai kamawa a cikin makon nan.

Bayanin ya kara da cewa gini da yake dauke da wannan agogo yana tsawon da ya kai mita 601, kuma fadinsa ya kai mita 251.

An gina wurin a kusa da masallacin ka'aba mai tsarki, wanda kuma agogo za ta zama daya daga cikin wadanda za a rika yin amfani da ita a duniya.

Wasu daga cikin injiniyoyin kasashen Jamus da Switzerland suka gina wurin tare da dora agogon, wadda an riga an gama saita ta, za ta fara bugawa a ranar daya ga watan Ramadan.

626662


captcha