Bangaren kasa da kasa; Alkur'ani mai tsarki hanya ce ta tattauna mahanga da tunani na al'ummomi duniya daban-daban, tare da fahimtar juna da kuma haduwa kan wasu abubuwa da suka hada 'yan adam baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar rasid ta kasar Saudiyya cewa, a cikin bayani da babban malamin addinin musluncin nan na kasar Saudiya kuma daya daga cikin jagororin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon (SAW) na kasar Sheikh Hassan Saffar ya yi ya bayyana cewa, kur'ani mai tsarki hanya ce ta tattauna mahanga da tunani na al'ummomi duniya daban-daban, tare da fahimtar juna da kuma haduwa kan wasu abubuwa da suka hada 'yan adam baki daya duk da banbancin akidunsu.
Sheikh Hassan Saffar ya bayyana cewa alkur'ani mai tsarki ya bayar da bayanan annabawa da al'ummoi daban-daban da aka yi a tarihin duniya, wanda hakan ke tabbatar da cewa kur'ani mai tsarki ya hada bayanan dukkanin al'ummomi da mahangarsu.
Kamar yadda ya tabbatar da cewa wannan littafi yana kira dukkanin 'yan adam zuwa ga abin da shine ya fi yin daidai da su a sha'anin rayuwar duniya, wanda kuma yin hakan tare da imani shi ne zai kai mutum zuwa samun rabo wajen ubangiji a rayuwa ta llahira.
626538