Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na turkishny cewa, wasu kungiyoyin kiristoci a kasar Amurka sun fito karar sun bayyana rashin amincewarsu da bayyana wata a matsayin ranar kone kur'ani mai tsarki ta duniya ba, bayan da wata majami'ar kasar Amurka ta masu tsananin gaba da addinin muslunci ta sanar da wata rana a matsayin ranar kone kur'ani ta duniya.
Bayanin ya zo bayan da gamayyar kungiyoyi kiristoci mabiya darikar protesting suka fitar da wani bayani na bai daya, inda suka ce ba wai kone kur'ani shi kansa bayyana wata rana kawai a matsayin ranar kone kur'ani babban zunubi a cikin akidar kiristanci.
Bayanin ya ce dole malaman majami'on kiristoci na duniya musamman ma na Amurka su dauki dukkanin matakan da suka dace wajen shiga kafar wando daya da irin wannan mummunar akida da ake dangantawa da addinin kirista.
Tuni dai musulmin kasar Amurka suka fitar da bayanai na nuna rashin amincewa da wannan mummanan mataki na majami'ar, tare da kiran mahukunta da su dauki matakin hana afkuwar hakan.
626480