IQNA

Taro Wakokin Musulunci A Yankin Chostan Na Kasar Rasha

15:19 - August 07, 2010
Lambar Labari: 1968476
Bangaren kasa da kasa; Ana shirin gudanar da wani babban taro wanda shi ne karo na uku da za a gudanar da shi a yankin cin gishin kai na Chostan na kasar Rasha da zai samu halartar wakilan kungiyoyin musulmi na kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da samu daga shafin sadarwa na yanar gizo na tatar-information an habarta cewa, ana shirin gudanar da wani babban taro wanda shi ne karo na uku da za a gudanar da shi a yankin cin gishin kai na Chostan na kasar Rasha da zai samu halartar wakilan kungiyoyin musulmi na kasar Rasha da kewaye.

Taron zai bayar da muhimmanci wajen bayyana matsayin tarihin addinin muslunci da dadaddun al'adunsa, da kuma wayar da kan musulmi kan muhimmancin yin riko da koyarwar addininsu a cikin dukkanin harkokin zamantakewar rayuwarsu.

Kungiyoyi da dama na musulmi masu gudanar da wakokin musulunci sun yi rijistar halartar taron, da nufin gabatar da wakokin muslunci na fadakarwa ga al'ummarsu.

627528



captcha