IQNA

Wilders Zai Halarci Taron Kiyayya Da Musulunci A Amurka

12:09 - August 08, 2010
Lambar Labari: 1969030
Bangaren kasa da kasa; Dan majalisar dokokin kasar Holland din nan mai tsananin kiyayya da addinin muslunci Geert Wilders ya bayyana cewa a shirye yake ya halarci taron nuna kyamar Musulunci da wasu kiristoci masu tsattsauran ra'ayi suka ce za su yi a Amurka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na duniyabulteni an bayyana cewa, dan majalisar dokokin kasar Holland din nan mai tsananin kiyayya da addinin muslunci Geert Wilders ya bayyana cewa a shirye yake ya halarci taron nuna kyamar Musulunci da wasu kiristoci masu tsattsauran ra'ayi suka ce za su yi a Amurka a lokacin gudanar da tarukan tunawa da harin 11 ga watan Satumba.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zanga-zanga dai masu tsattsauran ra'ayin za su gudanar da ita ne domin nuna kyamarsu da addinin Musulunci, musamman ma gina wani babban masallaci a birnin New York.

Tun kafin wannan lokacin da gwamnatin Amurka da ma mahukuntan birnin New York gami da dukkanin bangarorin gwamnati da abin ya shafa sun nuna amincewarsu da batun gina masallacin, amma masu gaba da Musulunci sun nuna rashin amincewa.

628113





captcha