IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Sauraren Karatun Kur'ani A London

12:04 - August 08, 2010
Lambar Labari: 1969034
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da silsilar zaman sauraren karatun kur'ani mai tsarki a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda za a gudanar a cikin watan Ramadan mai alfarma tare da halartar makaranta kur'ani daga sassa daban-daban na kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ic-el an habarta cewa, za a gudanar da silsilar zaman sauraren karatun kur'ani mai tsarki a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda za a gudanar a cikin watan Ramadan mai alfarma tare da halartar makaranta kur'ani daga sassa daban-daban na kasar ta Birtaniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa, za a gudanar da zaman sauraren karatun kur'ani a kowace rana kafin sallolin magriba da isha'i a cikin watan mai alfarma.

Shugaban cibiyar kula da harkokin muslunci ta birnin London Mohammad said Bahmanpour shi ne zai jagoranci gudanar da zaman sauraren karatun kur'anin.

627821


captcha