IQNA

An Fara Kiraye-Kiraye Da A 'Yantar Da Ka'aba Daga Wahabiyawa

12:03 - August 08, 2010
Lambar Labari: 1969036
Bangaren kasa da kasa; Wasu masana tarihin muslunci da masu kare hakkokin dan adam na kasashen muslmi da dama gami da wasu kasashen larabawa, sun yi kira da a karbe tafiyar da lamarin Ka'aba da masallacin manzon Allah daga hannun wahabiyawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na sadarwa na alalam an habarta cewa, wasu masana tarihin muslunci da masu kare hakkokin dan adam na kasashen muslmi da dama gami da wasu kasashen larabawa, sun yi kira da a karbe tafiyar da lamarin Ka'aba da masallacin manzon Allah daga hannun wahabiyawa da suka mamaye lamarin tafiyar da wuraren biyu masu tsarki.

Bayanin ay ci gaba da cewa masanan sun gudanar da zama ne na musamman kan hakan, inda suka bukaci duniyar musulmi da ta mike tsaye wajen kubutar da wadannan wurare masu tsarki daga hannun mutane masu gurbatacciyar akida kan addinin Musulunci.

Tun bayan da turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya suka dora 'yan gidan Sa'ud kan karagar sarautar saudiyya, tare da nada Mohammad Bin Abdulwahab a matsayin malamin gidan sarautar, masu akida irin tasa suke rike da wurare masu tsarki na kasar Hijaz.

627966


captcha