Bangaren kasa da kasa; Jami'ar Al-mostafa (SAW) tana hanyoyi da daman a bunkasa harkokin ilmi a cikin kasashen musulmi, kuma ahalin yanzu akwai karanci cibiyoyin addinin Musulunci a cikin wasu kasashen musamman ma wadanda ban a musulmi ba.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, sheikh Kasim shugaban cibiyar rasul a'azam a kasar Thailand ya bayyana cewa, jami'ar Al-mostafa (SAW) tana hanyoyi da daman a bunkasa harkokin ilmi a cikin kasashen musulmi, kuma ahalin yanzu akwai karanci cibiyoyin addinin Musulunci a cikin wasu kasashen musamman ma wadanda ba na musulmi ba ke cikin nahiyar Asia.
Malamin ya ci gaba da cewa ya kamata jami'ar Al-mostafa (SAW) ta kara maida himma wajen bude wasu cibiyoyin a cikin irin wadannan kasashe sakamakon karancin wuraren gudanar da harkokin addinin Musulunci, tare da bunkasa cibiyoyin da ke akwai a halin yanzu.
A bangare guda ya yaba da irin rawar da wannan jami'a take takawa wajen habbaka harkokin ilmin addinin Musulunci a cikin gida da kuma kasashen ketare.
640715