IQNA

Za A Gudanar Da WaNi Taron Iraniyawa Daliban Jami'a A Malazia

12:38 - August 29, 2010
Lambar Labari: 1983066
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani raon kur'ani na daliban jami'a a Iraniyawa kasar malazia, a jami'ar UTM da ke birnin Kualampour fadar mulkin kasar Malazia a cikin wannan mako da muke ciki.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kasar Malazia an habarta cewa, za a gudanar da wani raon kur'ani na daliban jami'a a Iraniyawa kasar malazia, a jami'ar UTM da ke birnin Kualampour fadar mulkin kasar Malazia a cikin wannan mako.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar mafi yawan dalibai Iraniyawa da suke a jami'oi daban-daban an kasar Malazia, inda za a gabatar da jawabai kan muhimmancin lizimtar umurnin kur'ania cikin rayuwar zamantakewa.

Daga cikin daliban har da wadanda suke gudanar da kwasa-kwasai a bangarori na ilimin likita da kuma dalibai a bangaren ilmomin kimiyya da fasaha.

643029




captcha