IQNA

Shirin Kur'ani Na Kasar Kuwait Ya Samu Karbuwa

11:32 - September 01, 2010
Lambar Labari: 1985728
Bangaren kasa da kasa; Shirin kasar Kuwait na kur'ani da aka bullo da shi domin watan Ramadan mai alfarma ya samu karbuwa matuka a tasakanin al'ummar kasar.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar kasar Kuwait ta Alkabs cewa, shirin kasar Kuwait na kur'ani da aka bullo da shi domin watan Ramadan mai alfarma ya samu karbuwa matuka a tasakanin al'ummar kasar ta Kuwait.

Bayanin ya ce shirin wanda babbar cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta kasar da ke karakashin ma'aikatar kula da ayyukan addini, ya samu karbuwa daga cibiyoyi raya ilmomin kur'ani da kuma kungiyoyi na makaranta.

Shirin ya kunshi hanyoyi na koyar da karatun kur'ani da kuma koyar da harda gami da ilmomin kur'ani mai tsarki ga matasa, ta yadda za su iya koyon abubuwa da dama bna kur'ani cikin kankanin lokaci.

645827
captcha