Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dilalncin labaran wam an habarta cewa, makarancin kur'ani mai tsarki dan kasar Algeria ya zo na daya a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa wato UAE.
Makarancin wanda daya ne daga cikin wadanda suka yi fice a tsawon lokacin da aka dauka ana gudanar da gasar, ya kasance daga cikin wadanda suka kai ga mataki na karshe na gasar.
645699