Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari daga kamfanin dilalncin labaran kuna cewa, an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a jiya a kasar Algeria wadda ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar ke daukar nauyin shiryawa a kowace shekara.
Ministan ma'aikatar kula da harkoki addini ta kasar Bu Abdullah Golamullah shi ne ya jagoranci taron bude gasar, yanzu haka dai wakilai daga kasashen duniya 43 ne suke halartar wannan gasa.
Bayan kammala gasar hardar kura'ni ta kasar alageria da ake gudanarwa a karo na bakwai a wannan shekara, za a bayar da kyautuka ga wadanda suka lashe gasar.
645681