IQNA

Shugaban Cibiyar Al'adu ta Kuwait Ya Kai Ziyara A Baje Kolin Kur'ani

22:54 - September 01, 2010
Lambar Labari: 1985865
Bangaren kasa da kasa; Shugaban cibiyar al'adu ta kasar Kuwait ya kai wata ziyara ta musamman a baje kolin kur'ani mai tsarki da ake guadanrwa a birnin Tehran fadar mulkin jamuriyar Musulunci.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban cibiyar al'adu ta kasar Kuwait ya kai wata ziyara ta musamman a baje kolin kur'ani mai tsarki da ake guadanrwa a birnin Tehran fadar mulkin jamuriyar Musulunci ta Iran.

Bayanin ya ci gaba da cewa, shugaban cibiyar al'adun ta kasar Kuwait ya zagaya zuwa bangarori daban-daban na baje kolin kur'anin, inda ya yaba matuka da yadda kasuwar take ci gaba da gudana a wannan lokaci na Ramadan.

Daga cikin bangarorin day a ziyarta har da bangaren da aka baje kayyakin kur'ani da suka danganci kanan yara, na koyar da su karatun kur'ani.

645397



captcha