IQNA

Za A Bude Wani Bangare Na Ayyukan Kur'ani Na Mashhad

22:54 - September 01, 2010
Lambar Labari: 1985866
Bangaren kasa da kasa; Za a bude wani bangare na kasa da kasa na ayyukan kur'ani da suka kebanci birnin Mashhad mai alfarma a baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa a wajen baje kolin kayyakin kur'ani na kasa da kasa a birnin Tehran an bayyana cewa, za a bude wani bangare na kasa da kasa na ayyukan kur'ani da suka kebanci birnin Mashhad mai alfarma a baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran fadar mulkin Iran.

Bayanin ya kara da cewa, wannan bangare zai nuna wasu daga muhimamn ayyukan kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a lardin Khurasan musamamn ma a birnin Mashad, inda zai bangaren da za a ci gaba da nuna irin wadannan kayyaki a kowace shekra a lokacin baje kolin na kasa da kasa da ake gudanarwa.


646001

captcha