Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habata cewa a wani bayani da yanakalto daga shafin sadarwa na OIC an bayyana cewa, Babban kwamitin fikihun Musulunci na duniya da ke da dangantaka da kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya bukaci musulmi da su aike da zakatul fitr da za su fitar zuwa ga al'aummar musulmi na kasar Pakistan da ambaliyar ruwa ta yi wa yankan kauna a cikin 'yan makonnin nan.
Suka kara da cewa bisa fatawar da malaman da ke cikin kwamitin suka fitar sun halasta mika wannan zakka da ake fitarwa a mika ta ga wadannan bayin Allah domin agaza musu.
Ba'ada bayan haka ma wasu da dama daga cikin malaman addinin Musulunci a kasashe daban-daban sun bayar da fatawar halasta mika zakkar fitr ga mutanen kasar Pakistan.
647002