Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar musulmin Rasha cewa, An gudanar da tarukan ranar Qods ta duniya a birnin Moscow fadar mulkin kasar Rasha a ranar Juma'ar da ta gabata domin karba kiran marigayi Imam na raya wannan rana.
Wadanda suka halarci tarukan sun yi ta rera taken yin Allawadai da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan palastinawa, da kuma neman yahudawan sahyuniya da su fice daga dukkanin yankunan palastinawa da suka mamaye.
Haka nan kuma sun jadda cewa masallacin Qods mai alfarma da ke karkashin danniyar yahudawan sahyuniya dole ne musulmi su yunkura domin 'yanto shi.
647602