Bangaren kasa da kasa; Jagorin musulmi da na mabiya addinin kirista a kasar Girka sun gudanar da wani zama a birnin Athen fadar mulkin kasar, a wani buda baki da musulmi suka kira dukkanin bangarorin biyu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar zaman da ake bugawa a kasar Turkiya cewa, jagorin musulmi da na mabiya addinin kirista a kasar Girka sun gudanar da wani zama a birnin Athen fadar mulkin kasar, a wani buda baki da musulmi suka kira dukkanin bangarorin biyu na kasar.
Bayanin ya ce bababr cibiyar musulmi da ke birnin Athen ita ce ta dauki nauyin shirya wannan buda baki na hadin gwiwa da nufin karfafa dangantaka tsakanin bangarorin musulmi da kuma mabiya addinin kirista da ke kasar Girka.
Da dama daga cikin mambobin kungiyoyin musulmi da na kiristoci a kasar ta Girka sun halarci wannan buda baki, kamar yadda wasu daga cikin jakadojin kasashen musulmi a kasar su suka halarta.
647550