Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da bangaren hulda da jama'a na cibiyar yada al'adu ta kasar Iran ya bayar an bayyana cewa, an gudanar da tarukan ranar Qods ta duniya a kasar Qatar wanda ofishin jakadancin jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Doha ya shirya.
Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar manyan malaman addini da kuma wasu fitattun masana na kasar, da suka hada sheikh Muhyiddin babban sakataren kwamitin masana musulmi na duniya, da kuma wasu malmaai.
Haka nan kuma taron ya samu halartar jakadojin wasu daga cikin kasashen da na latin Amurka, da suka hada da Afghanistan, Turkiya, Iraki, Bangaladash, Venzuela, Brazil, Cuba, yeman, da sauransu.
647270