IQNA

An Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Matasa A Kasar Yeman

13:53 - September 06, 2010
Lambar Labari: 1988704
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wata gasar hardar kur'ani mai tsarki da ta kebanci matasa a mai taken himma domin tarbiyantar da matasa kan koyarwar kur'ani da cibiyar kula da ayyukan kur'ani kur'ani ta birnin And ta dauki nauyin shiryawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na saba na yanar gizo an bayyana cewa, an gudanar da wata gasar hardar kur'ani mai tsarki da ta kebanci matasa a mai taken himma domin tarbiyantar da matasa kan koyarwar kur'ani da cibiyar kula da ayyukan kur'ani kur'ani ta birnin And ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.

An raba bangarorin gudanar da gasar ne zuwa kashi uku, domin bayar da dama ga dukkanin wadanda suka hardace wani bangare su iya shiga cikin shirin gasar kuma su kara samun karfin gwiwa wajen ci gaba da hardar.

Akwai wadanda suka gudanar da hardar a bangare juzu'i na daya zuwa goma, da kuma juzu'i na goma zuwa ashirin, daga na kuma zuwa abin da ya yi sama.

648236



captcha