IQNA

An Fitar Da Kwanan Watan Musulunci Na Shekarar 2011 A Rasha

14:18 - September 06, 2010
Lambar Labari: 1988711
Bangaren kasa da kasa; An fitar da kwanan watan shekarar Musulunci ta 2011 a kasar Rasha, kuma an rubuta kalandar ne da harshen rashanci, wanda cibiyar yada addinin muslunci ta Iman ta dauki nauyin bugawa da fitarwa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari daga shafin sadarwa na yanar gizo na info-islam cewa, an fitar da kwanan watan shekarar Musulunci ta 2011 a kasar Rasha, kuma an rubuta kalandar ne da harshen rashanci, wanda cibiyar yada addinin muslunci ta Iman ta dauki nauyin bugawa da fitarwa domin amfanin musulmin kasar.

Wannan kalanda da ke dauke da kwanan watan shekarar Musulunci tana da tarihin dukkanin shekarun biyu na Musulunci da kuma miladiyya, inda ta ke kawo muhumman abubuwan da suka faru a cikin addinin Musulunci tare da cikakken kwanan wata.

648250














captcha