IQNA

Wata Mata Bafalastiniya 'Yar shekaru 74 Ta Hardace Kur'ani

14:22 - September 06, 2010
Lambar Labari: 1988725
Bangaren kasa da kasa; Wata mata 'yar shekaru 74 ta samu sa'ar hardace kur'ani mai tsarki a yankin zirin gaza Palastinu, wadanda da dama daga cikin matasa suka kasa yin hakan.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga wani shafin sadarwa na harshen larabci Muhit a yanar gizo an bayyan acewa, wata mata 'yar shekaru 74 ta samu sa'ar hardace kur'ani mai tsarki a yankin zirin gaza Palastinu, wadanda da dama daga cikin matasa suka kasa yin hakan saboda rashin dacewa.

Bayanin ya ce wannan mata ta dauki dogon lokaci tana halartar karatun kur'ani na bai daya da ake yia wani masallaci da ke yankin tun tana da sauran kuruciyarta, amma a lokacin ba ta da niyar yin harda, amma bayan da shekarunta suka nisa sai ta yanke shawarar shiga hardar kur'ani, kuma ta samu dacewa da hakan.

648444









captcha