IQNA

Taron Goron Sallah Karama Ga Kowa A Kasar Belgium

13:44 - September 07, 2010
Lambar Labari: 1989661
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro na idin karamar salla a birnin Brussel na kasar Belgium da aka baiwa taken goron salla ga kowa, wanda za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa tare da halartar wakilan cibiyoyi daban-daban na musulmi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na Islamic-events cewa, za a gudanar da wani zaman taro na idin karamar salla a birnin Brussel na kasar Belgium da aka baiwa taken goron salla ga kowa, wanda za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa tare da halartar wakilan cibiyoyi daban-daban na musulmin kasar.

Babbar manufar gudanar da wannnan zaman taro ita ce kara wayar da kan mutanen da suka karbi addinin Musulunci ba da jimawa a kasar, da kuma sauraren bayanansu kan dalilan da suka sanya su suka karbi addinin Musulunci.

Haka nan kuma an aike da goron gayata ga wasu kungiyoyi na wadanda ba musulmi ba domin su halarci, kamar yadda wasu kungiyoyin musulmin kuma za su bayyana irin ayyyukan da suke gudanarwa a kasar na addinin muslunci.

649571



captcha