IQNA

Tunanin Wahabiyanci Ya Fara Samun Wuri A Jami'ar Azhar

13:45 - September 07, 2010
Lambar Labari: 1989663
Bangaren kasa da kasa; Babban malamin nan kuma marubuci kuma malamin ilimin kalami da falsafa a jami'ar Azhar Ahmad Abdulrahim ya bayyana cewa, tunanin akidar wahabiyanci ya fara samun wurin zama a cikin jami'ar Azhar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na shia today.com an bayyana cewa, babban malamin nan kuma marubuci kuma malamin ilimin kalami da falsafa a jami'ar Azhar Ahmad Abdulrahim ya bayyana cewa, tunanin akidar wahabiyanci ya fara samun wurin zama a cikin jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar.

Bayanin ya ci gaba da cewa malamin ya nuna matukar takaicinsa dangane da yadda tunanin wahabiyanci ya fara samun wurin zama a cikin jami'ar Azhar, wadda ta ginu a kan fahimtar juna tsaknain dukkanin ilmomi na Musulunci ba tare da kyamar wani ba.

Ya ce tun sama da shekaru goma da suka gabata ne irin wannan tunani na wahabiyanci tare da kyamar wani bangaren musulmi ya fara yin tasiri a cikin wannan babbar jami'a ta Musulunci.

649307



captcha